Min menu

Pages

Yanzu yanzu :- An sake kai mummunan hari Isra'ila

 Yanzu yanzu :- An sake kai mummunan hari Isra'ilaYanzu-yanzu an kashe mutum 10 a harin rokokin da kungiyar Hamas ta kai wa Isra'ila


Jami'an lafiya a Isra'ila sun ce an kashe mutum 10 a harin rokokin da ya tarwatsa wani gini a Ramat Gan a birnin Tel Aviv.


An ambato hukumomin tsaron Isra'ila na cewa an kai harin roka biyu kuma mutane da dama suka jikkata.


An kuma bayar da rahoton wasu hare hare a Rishon Lezion da kuma Taibe na Larabawa kusa da Tel Aviv, amma babu tabbas ko an samu hasarar rai ko jikkata kawo yanzu.


Wannan dai shine hari mafi muni da kungiyar Hamas ta kaiwa Isra'ila.


Kuma wasu na ganin cewa wannan nasara da kungiyar Hamas ta samu bai rasa nasaba da lalacewar batirin Na'urarar kakka6o rokoki ta Isra'ila wadda ake kira"Iron Dome" a turance.


Ita dai wannan na'ura itace ta taimaka wajen kakka6o kashi 90 cikin dari na rokokin Hamas take harbawa.

Comments