Min menu

Pages

Kasar Isra'ila ta harba roka a Ofishin gidan jaridar Al-Jazeera saboda wannan dalilin

Kasar Isra'ila ta harba roka a Ofishin gidan jaridar Al-JazeeraYanzu-yanzu kasar Isra'ila ta jefa wata roka kan Ofishin gidan jaridar Al-jazeera dake fallasa irin cin zarafin da take yi wa Palasdiwa musulmai.


Kasar Isra'ila dai tana zargin gidan jaridar na Al-jazeera da taimawa musulmai Palasdiwa ne wajen sanar da duniya halin da su ke ciki.


Masana harkokin yaki sun bayyana cewa wannan wani sabon makirici ne kasar Isra'ila ta shirya domin ci gaba da kisan musulmai Palasdiwa ba tare da duniya ta san halin da su ke ciki ba.


Gidan jaridar Al-jazeera shine gidan jarida kadai dake bibbiyar adadin mutanen da kasar Isra'ila ta kashe a kasar Palastine.


Kuma  kawo yanzu Palasdiwa 150 aka kashe a wannan rikici.Comments