Min menu

Pages

Yanzu-Yanzu Abdulsalam Abubakar ya mayar da martani kan zargin da jama'a ke masa na ta'addanci

 Yanzu-Yanzu Abdulsalam Abubakar ya mayar da martani kan zargin da jama'a ke masa na ta'addanci 


An kama jirgi mallakin tsohon shugaban kasar Nijeriya dauke da makamai za'a kaiwa yan bindiga


"Jama'a kar ku yarda da labarin da ake yadawa cewa an kama wani jirgin sama mai kai wa 'yan bindiga abinci da makamai a jihar Neja mallaki na".


Tsohon shugaban kasa Abdulsalam Abubakar ya karyata labarin da ake yawo da shi cewa an cafke wani jirgin sama mai saukar ungulu wanda ake zargin yana kai wa 'yan bindiga kayan abinci da kuma kayan yaki a jihar Neja.


Abulsalam ya bayyana cewa "wannan labari ba gaskiya bane, sannan kada kowa ya yarda da wannan labari. Domin labari ne wanda aka kirkira don a bata min suna".


Tun jiya dai ne ake ci gaba da yada wannan labari wanda aka alakanta Abdulsalam da shi.


Daga karshe tsohon shugaban kasar ya roki Allah ya kawo wa ma Najeriya zaman mai dorewa.


Daga: Dr Yakubu Sulaiman Media Aid to Abdulsalan Abubakar

Comments