Min menu

Pages

Yanzu Nijeriya nada cikakken tsaro:- LAI MUHD

 Yanzu Nijeriya nada cikakken tsaro:- LAI MUHD
Ministan yada labarai da al’adu na Najeriya Lai Mohammed ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa duk da matsalolin tsaro da kasar ke fuskanta a yanzu, Najeriya na cikin aminci.


Kai mohammed, wanda ya bayyana hakan lokacin da ya karbi bakuncin Oluyin na Iyin-Ekiti, Mai Martaba, Oba Adeola Adeniyi Ajakaiye, ya jaddada bukatar shugabanni a dukkan matakai su bai wa mutane sakon bege maimakon yin kalaman da za su iya ta’azzara tashin hankali.


Ministan ya lura cewa sarakunan gargajiya na da matukar muhimmanci wajen wanzar da zaman lafiya da tsaro a yankinsu kuma bai kamata a yi biris da su ba.


Ya roki masarautar da ta yi aiki tare da takwarorinsa sarakunan gargajiya, da kuma Gwamnatin Jihar Ekiti, don tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar.


Ministan ya fada wa basaraken cewa gabanin ziyarar tasa zuwa Kogon Esa da Okuta Abanijorin, ma’aikatar za ta tura Hukumar Kula da Gidajen Tarihi (NCMM), wata ma’aikatar kula da gidajen tarihi da wuraren tarihi a kasar, don ziyartar wasu wuraren yawon bude ido guda biyu a Iyin-Ekiti – Kogon Esa da Okuta Abanijorin – sannan su kawo masa rahoto.


Ya tabbatar wa Oluyin cewa gwamnati za ta yi iya kokarinta don taimakawa da nunawa da kuma fadada manyan wuraren yawon bude ido guda biyu a garin, ya kara da cewa sanya wuraren yawon bude ido a kan taswirar kasa da ta duniya zai jawo hankalin masu yawon bude ido, wanda hakan, zai bunkasa tattalin arziki.

Comments