Min menu

Pages

WATA AL'ADA:-Inda yan mata suke nuna jikinsu domin su samu mazan aure

 Abin mamaki dai baya karewa idan kana yawo zaka rika gamuwa da abubuwa iri iri a yau cikin shirin namu muna tafe ne da bayanin wata kabila wacce matan ciki ke nuna jikinsu idan suna neman mazan aure.


Koda yake ko wacce kabila sunada irin al'ada wacce suka rika iyaye da kakanni wacce suke gabatar da ita tsawon lokaci.Dan haka yau gamu dauke da labarin wata kabila wacce suka riki al'ada ta nuna jikinsu idan suna son samun mijin aure.


Matan ko kuma ince yan matan suna bayyana jikinsu ne tsawon sati uku idan suna son samun mazan da zasu aure su.


Bayan sunyi haka kuma sukan sake samun wata doguwar ciyawa su daura a jikin kayansu sannan su fita suna zagayawa gari suna rawa.


Sauda dama tsofin yan mata ko kuma zawarawa sukan shiga cikin yan matan domin su nuna jikin nasu.


Sunan wannan kabilar dai ashenda sune ke gabatar da irin wannan al'ada daga zarar yara mata sun fara isa aure.


Suna zaune ne a wasu yankuna na kasar Ethiopia.

Comments