Min menu

Pages

WATA AL'ADA Da ake cinye mutum idan ya mutu maimakon a binne shi

 Kabilar da suke cinye mutum idan ya mutu maimakon su binne gawar.



Al'umomi sun kasu kashi kashi cikin wannan duniyar haka kuma tsarin al'ada da dabi'un kowacce kabila yasha bamban dana wata kabilar.


In kana karanta labarai ko kana yawo cikin duniya zaka rika gamuwa da abubuwa kala kala na ban mamaki masu tarin yawa.


Wasu abubuwan su birgeka wasu su baka haushi wasu ma dariya zasu baka, domin ganin abin zakai wani iri domin kai a taka al'adar ba'a irin haka.


Wata al'ada nazo muku da ita, ta wata kabila dake wata kasa a cikin duniya, inda su basu yarda su binne gawar dan uwansu ba idan ya mutu saidai su yayyanka naman jikinsa ko jikinta su cinye suna kuka.


Kabilar yanomami wata kabila ce dake zaune can wani yanki mafi nisa a wani layi da ya hada kasar Venezuela da Brazil.


Kabilar yanomami sun samo asali ne tun can wajen shekarar 1759.


Su dai wannan kabilar kwata kwata basu amince su binne dan uwansu ba idan ya mutu saidai su yanka namansa su gasa su rarraba sannan su cinye.

Comments