Min menu

Pages

Idan ban auri gwamna Tambuwal ba zan iya rasa raina inji wata budurwa

 TIRKASHI!Idan ban auri Gwamna Tambuwal ba sai dai na fada rijiya~ Inji Wata budurwa


Wata budurwa tsaleliya daga jihar Kebbi mai suna Hafsat Umar ta bayyana irin yadda take matukar son Gwamnan jihar Sokoto R.t Aminu Waziri Tambuwal da aure.


Matashiyar ta bayyana cewa a rayuwar ta bata taba kamuwa da son wani 'da namiji ba kamar yadda ta kamu da son Gwamnan jihar Sokoto R.t Aminu Waziri Tambuwal.


Matashiyar ta ci gaba da cewa, ita a yanzu batada wani buri a rayuwar ta kamar yau ace ta yi ido hudu da sahibin ta R.t Aminu Waziri Tambuwal ba.


To sai dai matashiyar ta bayyana cewa bata san ta wace hanya zata bi ba wajen ganin ta hadu da Gwamna Tambuwal ba.


Saboda haka ne ta yanke shawarar tattaunawa da wakilin mu domin kai koken ta ga Gwamna Aminu Waziri Tambuwal.


Saboda haka muna fatar Allah yasa wannan sako ya isa ga Gwamna Tambuwal.


Tabbas masoyi abin so duk yanda yake.

Comments