Min menu

Pages

WATA AL'ADA:- Da ake kone duk wata mata tare da mijinta idan ya rigata mutuwa

 WATA AL'ADA:- Da ake kone duk wata mata tare da mijinta idan ya rigata mutuwa


Assalamu alaikum ma'abota bibiyarmu a wannan gidan na duniyar labarai, barkanmu da wannan lokacin sannan sannunmu da sake haduwa tare daku.


Hakika muna jin dadin kasancewar ku tare damu dan haka muna godiya sosai da sosai.


Kamar yadda duniya keda girma tare da fadi da yawan mutane masu yare da dama hakan yasa aka samu al'adu iri iri cikin kowacce kabila.


Yau idan Allah ya yarda muna tafe ne da labarin wata kabila masu wata al'ada mai abin mamaki.


Ita dai wannan kabila suna kone duk wata mata ne da mijinta ya mutu tare da gawar mijin nata..


Shekaru da yawa cikin wannan kabilar mata basu da wata daraja ko kadan duk wani abu daya faru sai kaga matan sune abin zargi da kuma wofintarwa ko kadan dan haka duk matar da mijinta ya mutu to alhakin kisan mijin nata na kanta.


Hakan shine yasa wannan kabilar basa yadda da duk matar da mijinta ya mutu dole tare da gawar mijin za'a hadata a kone da matar tasa.


Sudai wannan kabilar sunanta sati ko kuma satee suna zaune ne acan kasar India wannan kabilar ita ce ke kone duk matar da mijinta ya mutu.


To jama'a kunji dai kadan daga tarihin wannan kabilar dan haka mu hadu a wani shirin domin samun wasu sabin labaran.


Mun gode

Comments