Min menu

Pages

Wani guri a Nijeriya wanda Naira dubu goma aura ma budurwa

 Wani yanki a Nijeriya wanda idan har kanada Naira dubu goma to zaka iya auren budurwaKoda yake mutane suna yin aure a gurarensu da matukar tsada inda za kuga mutane sun kashe kudade masu yawa idan har za suyi aure.

Karanta:- kabilar da maza ke canjen matansu zuwa ga wani mijin

Tun kama daga kan kudin da zasu bewa mata da sunan sayen baki da kuma kudin an gani ana so da kayan lefe dadai sauran su.


Wannan yasa samari da dama kan jimawa kafin su samu suyi aure saboda basu kudaden da zasu yi irin wadannan abubuwan.


Dan haka sai kuga tarin samari masu yawa ba tare da sunyi aure ba saboda tsananin tsadar da aure yake dashi a yankin da suke.


To saidai tace wani yanki can a Nijeriya abin ba haka yake ba domin saurayi nada damar da zai auri zankadediyar budurwa idan yanada naira dubu goma kacal.


Becheve shine sunan yankin dake cikin Obanliku yanada girma tare da tara mutane.


A wannan yankin babu wani kudi da ake kashewa idan mutum zaiyi aure domin duka baifi ya kashe dubu goma ba zai samu mata saidai dan abinda baza a rasa ba idan auren ya kusa.


Yan matan yankin basu son a hada su aure da tsoho sunfi son samari.

Comments