Min menu

Pages

TURƘASHI | Mijinta Ya Saketa Saboda Taje Karɓar Kayan Tallafin Sallah Ba Tare Da wannan dalilin ba

 TURƘASHI | Mijinta Ya Saketa Saboda Taje Karɓar Kayan Tallafin Sallah Ba Tare Da Izninsa BaWani abin al'ajabi ya faru da wata mata wacce ba sai mun bayyana sunanta ba, inda matar ta fita ba tare da izinin mijinta ba taje wajen da ake raba kayan tallafin Sallah domin itama ta karɓi nata rabon.


Majiyar mu ta shaida mana cewar, kwatsam sai mijin nata ya ganta a wajen da ake rabon kayan, sai ya tambayeta "shin banyi miki kayan Sallah ba da ke da yara?" Nan fa ta amsa masa da cewar yayi musu, nan take yace kada ta koma masa gida ya saketa.


Wannan al'amari dai ya faru ne a ranar Litinin a Ƙofar Sarki ta garin Dukku dake jihar Gombe.


Comments