Min menu

Pages

Babu fashi za muyi sallah yau inji Sheikh Dahiru Bauchi

 Babu fashi za muyi sallah yau inji Sheikh Dahiru BauchiMuna sanar da daukacin mabiyan darikar tijjaniyya cewar babu fashi yau take sallah sakon shugaban Kungiyar kenan ga mabiyansaTun jiya ake ta cece kuce akan ganin wata inda majiya mai karfi daga fadar mai martaba sarkin musulmai ya sanar da cewar ba a ga jinjirin watan shawwal din ba dan haka sallah sai ranar alhamis.


To ana haka ne sai aka ji wata sanarwa daga bangaren shugaban Kungiyar darikar tijjaniyya cewar a tashi da sallah ranar laraba saboda tabbatuwar ganin watan da suka ce anyi a wasu garuruwa a kasar.


To daga baya kuma sai aka kuma cewa wai shugaban darikar tijjaniyya din yace ayi amfani da maganar sarkin musulmai.


Amma kuma sai muke sake samun labarin cewa ta tabbata a tashi da sallah yau inji Sheikh Dahiru Bauchin


Allah shine masani

Comments