Min menu

Pages

DA DUMINSA:- Kuyiwa sarkin musulmai biyayya ku tashi da azumi gobe sabon sako daga gun sheikh Dahiru Bauchi

 DA DUMI-DUMI Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya ce ayiwa Sarkin Musulmi biyayya a acigaba da Azumi Sallah sai ranar Alhamis kuma ya musanta labarin da ake yadawa cewa ya ce ayi sallah gobe Laraba A tattaunawa da manema labarai wasu makusantan Shehu sun tabbatar da cewa bara ne ya fitar da sanarwa kuma a wancen lokacin yayi sanarwar ne a cikin Bidiyo amma a bana bai yi ba, "saboda haka duk wanda ya ce Shehu yace a ajiye Azumi gobe to ya nuna maku hujja cikin bidiyo ko sautin murya"


Wannan dai ya kawo karshen kokarin amfanin da sunan Shehin malamin da wasu ke son yi wajen kawo rarrabuwa a addinin musulunci musamman kokarin tunzura wasu su ajiye Azumi Gobe bayan Sarkin Musulmi na Nigeria Alhaji Sa'ad Abubakar III ya tabbatar da cewa ba a ga watan sallah ba don haka ayi Azumi gobe Laraba sai ranar Alhamis ayi bikin idin sallah karama.

Comments