Min menu

Pages

Shin kunsan dan fashi na farko a tarihin Nijeriya? Kunsan ya gagari jami'an tsaro da hukuma?

 Shin kunsan dan fashi na farko daya fara fashi da makami a tarihin kasar Nijeriya?Barka da zuwa duniyar labari gidan da suke kawo muku labarai kala kala na da wanda suka faru a zamanin baya da kuma wanda suke faruwa yanzu.


Wannan gidan suna kawo tarihi na mutanen da suka shude da tarihin birane da halittun dake rayuwa a duniya walau na ruwa da na kan tudu.


Yau cikin ikon Allah zamu kawo muku labarin wani gagarumin dan fashi ne da aka taba yi a Nijeriya wanda ya gagari jami'an tsaro da mutane masu yawa.


Ance wannan barawon ya jima yana aikata ayyuka marasa kyau yayi sata kala kala ya dauke kayan mutane masu yawa amma an kasa.


A takaice dai a tarihin Nijeriya daya daga cikin manyan yan fashi da aka taba yi shine Ishola Oyenusi shine ya gabatar da hare hare mafiya muni da sunan fashi.


Ana fada masa suna Dr Oyenusi bawai dan yayi karatun Dr ba a'a saboda so da kaunar da yake yiwa karatun ne yasa ya juye ya koma wannan sunan duk da baiyi wani karatu mai yawa ba saboda ya tsaya ne tun a karatun sakandire


Daga karshe ya koma harkar fashi ne saboda mahaifansa basu biya masa kudin da zaici gaba da karatu ba.


Sata ta farko daya taba yi shine yin awun gaba da wata mota wanda ya kashe mai ita ya kwace saboda budurwarsa tana son kudi kuma bashi da kudin a lokacin.


Daga karshe suka saida motar Naira 400 a wancan lokacin sannan ya bewa budurwarsa kudin.

Yana shiga har banki da rana yayi fashi ba tare da ya kamu ba.

Yan sanda sunyi sunyi su kamashi amma dake hatsabibi ne bai kamu ba.


Ance a lokacin da dubun nasa ta cika da budurwar da yake so aka hada baki ta basu sirrin aka kamashi.

Comments