Min menu

Pages

DA DUMI DUMINSA:- Kungiyar boko haram ta raba kudin azumi ga al'ummar yobe da borno

 DA DUMI DUMINSA:- Kungiyar boko haram ta raba kudin azumi ga al'ummar yobe da borno.Kungiyar boko haram ta rarraba abubuwa masu yawa ga mutanen yobe da borno a matsayin tallafin watan ramadan.


Abubuwan da Kungiyar ta raba sun hadar da kudi, shinkafa, wake taliya gero da kuma masara duk a cewarsu tallafin watan ramadan dinne.


Yan tawayen daga kungiyar ta boko haram da suke samun goyon baya daga babbar Kungiyar da suke mata suna da kungiyar islama ta yammacin afrika wato ISWAP  sun raba kayayyakin tallafin watan ramadan a yankin jihar yobe da kuma borno.


Inda majiyar tace abubuwan da Kungiyar ta raba sun hadar da kudi da kuma kayan abinci irinsu shinkafa wake da kuma gero harda masara da kuma dawa dadai saurar abubuwa ga mazauna yankin.


Ko kwanan baya munji labarin yan Kungiyar na bayar da kudi ga samari tare da yi musu tayin suzo su shiga cikin tafiyarsu.

Comments