Min menu

Pages

Munanan Ɓarna Guda 12 Da Isra'ila Ta Yi Wa Falasɗinawa A Zirin Gaza Cikin Kwanaki bakwai Kacal

 Munanan Ɓarna Guda 12 Da Isra'ila Ta Yi Wa Falasɗinawa A Zirin Gaza Cikin Kwanaki bakwai Kacal— Ta harba Rokoki guda 1050

— Ta kashe mutane 139

— Ta Raunata Mutane 1000


Duk wannan abubuwan da na lissafa a sama da wannan zan faɗi a kasa sun faru ne daga Ranar 10/05/2021 zuwa yau 15/05/2021. Gwamnatin ƙasar Falasɗin ta tabbatar da wannan a wata takardan Sanarwa Manema labarai da ta fitar wanda tace adadin asarar da Isra'ila ta mata yakai na Dala Miliyan 155


1. Unguwanni na zaman mutane guda 719 suka lalata tare da tarwatsawa.


2. Gidaje 4271 aka rusa rugu-rugu.


3. Manyan gine-gine masu hawa 10 zuwa sama guda 76 suka rusa har ƙasa.


4. Ofisoshin gwamnati guda 63 aka ƙona ƙurmus zuwa toka.


5. Makarantu da Ɗakunan shan Magani guda 34 suka rusa cikin lokacin


6. Gidajen TV da Radiyo gami da ƙananun tashoahin sadarwa guda 23 aka rusa


7. Filayen Noma da wajajen kiwo da ya kai na kuɗi Dala Miliyan 10 suka lalata.


8. Guraben Tattalim Arziki da suka shafi Bankuna 4 da kasuwanni da suka kai darajar Dala Miliyan 20 suka lalata.


9. Sama da Motoci Mallakin mutane guda 120 aka lalata wanda kuɗin su ya kai Dala Miliyan 5.


10. Mummunan taadin da aka yiwa Mattaran wuta da makamashin su ya kai asarar kuɗin da yakai dala Miliyan 100.


11. Hanyoyi da wajajen shakatawa da abubuwan more rayuwa da aka lalata yakai na Dala Miliyan 13.


12. Manyan Masallatai 2 an rusa su duka sannan kusan guda 17 an lalata su, kuɗin su yakai Dala Miliyan 1.

Comments