Min menu

Pages

A shirye muke mu kafa sabuwar majalisar Dunkin duniya ta kasashen musulmi saboda irin wadannan abubuwan da ake mana inji Erdogan

 A shirye muke mu kafa sabuwar majalisar Dunkin duniya ta kasashen musulmi saboda irin wadannan abubuwan da ake mana inji  —ErdoganShugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyib Erdogan, ya bayyana cewa tunda majalissar ɗinkin duniya, ba za ta iya share hawayen ƙasashen Musulmin duniya ba to bata da amfani suci gaba da zama a cikinta, duba da yadda ake ta hallaka musulmin ƙasar Palasɗinawa, wanda Isra'ila ke yi amma ba tare da majalissar ɗinkin duniya ta ɗauki wani mataki na hana faruwar hakan ba.


In ji Erdogan, ya zama wajibi mu kafa sabuwar majalissar ɗinkin duniya ta (Muslim United Nations? domin kuwa abubuwan da ake yi na kisan musulmi tare da aibata su da sunan ƴan ta'adda hakan ba abun da zamu kyale bane, in ji shi, a wani jawabi da yayi a daren jiya a kafar talabijin ɗin kasar.


Kunji fa shin kuna goyon bayan ɗaukar wannan  mataki kuwa?


Muna fatan Allah ya taimaki wannan bawa na sa dake son kare addinin Musulunci da Musulmi ameen.

Comments