Min menu

Pages

Magidancin ya koka kan yadda matarsa taki hada shimfida dashi saboda wannan dalilin a cewarsa

Matata taki yarda mu hada shimfida inji wani magidanciWani Magidanci da ya gaza bayyana sunan shi, ya koka kan yadda matar shi ta kaurace wa kwana tare da shi sakamakon abinda ta ce ya ƙi korar mai gadin su.


Kawo yanzu kimanin makonni uku kenan da matar tashi ta ƙi hada shimfida da shi ba kamar yadda ya bayyana.


Ya ce "Matata ta ƙi haɗa shimfida da ni saboda na ki korar mai gadin mu"


To sai dai ya ce ba abu ne mai yiwuwa a ce ya kori mai gadin ba sakamakon irin biyayya da kyautatawa da yake gano daga gare shi, wanda kuma da ma ya kasance da mai gadin tun gabannin auren matar tashi.


A cewar kimanin shekara sha uku kenan yana tare da mai gadin, yayin da ita kuwa shekarar ta shida kenan kachal a gidan shi, don haka bai ga dalilin da zai sa ta raba su ba.


Ya kara da cewa kawo yanzu ba ta bayyana Mishi dalilin ta na cewa dole sai an kore shi ba, to amma ya fahimci cewa akwai rashin jin dadi a tsakanin ta da shi.


Ya ce a Yanzu haka Ƙwaƙwalwar shi ta rikice tare da rasa yadda za ta yi da lamarin.


Sau da dama dai ana samu saɓanin tsakanin matar gida da yar aiki, to amma wannan karon abun ya zo a kaikaice.

Comments