Min menu

Pages

An kama wani gardi da hijab a sahun mata a masallaci

 An kama wani gardi da hijab a sahun mataKungiyar yan banga tayi nasarar cafke wani gardi da yasa hijab ya shiga sahun mata a masallaci.


Lamarin ya auku ne a unguwa uku yan awaki kamar yadda rohoton yazo mana.


Wata matashiya ta tafi masallaci da wayarta to amma tana dubawa sai taga bata ga wayar ba wannan lamarin yasa ta fara zargin ko wacce sukai sahu da ita ne ta dauka to saidai bata ganta ba.


Acan gefe guda kuma yan banga sun hangi wani yana yana kokarin cire kaya da suka je sai sukaga kayan mata ne a jikinsa.


Saida aka bincika sai akaga shine ya dauki wannan wayar kuma shine sukai sahu tare da wannan budurwar da aka dauke mata waya.

Comments