Min menu

Pages

Kwana daya da shigar sabon shugaban hafsan sojoji dubi yadda ya fara nasara akan yan boko haram

Kwana daya da shigar sabon shugaban hafsan sojoji dubi yadda ya fara nasara akan yan boko haramKwana daya da shigar sabon shugaban Hafsan sojin Najeriya Faruku Yahaya Ofis, sojojin Najeriya sun fatattaki mayakan boko haram tare da kashe su a garin Rann


Kwana daya da shigar sabon shugaban Hafsan sojin Najeriya Faruku Yahaya Ofis, mayakan kungiyar boko haram sun yi yunkurin kai mummunan hari wanda basu taba kai irin sa ba a garin Rann dake karamar hukumar Kala Balge dake jihar Borno, inda hidikwatar "Operation Hadin Kai" take.


To sai dai zaratan sojojin Najeriya karkashin jagorancin sabon shugaban Hafsan sojin Najeriya Faruku Yahaya sun mayar da martani nan take, inda suka hallaka wadannan mayaka na kungiyar boko haram tare da kwato kayan yaki marasa adadi daga hannun su.


Sojojin sun samu nasarar kwace wasu manya manyan bindigogi masu kakkabo jiragen sama da kuma wasu AK-47 tare da lalata wata motar yaki ta su.


Hakama, sojojin sun tabbatarwa al'ummar garin na Rann cewa su kwantar da hankalin su, daga yanzu babu wani dan ta'adda da zai sake kusanto wannan gari ya tsire da ransa.


Comments