Min menu

Pages

Kasar Isra'ila na gaf da dandana kudar ta~Inji Erdogan

Ran maza ya baci:  Kasar Isra'ila na gaf da dandana kudar ta~Inji Erdogan Yanzu-yanzu shugaban kasar Turkiyya Racep Tayyip Erdogan ya bayyana cewa" Wallahi za mu koyawa kasar Isra'la darasi a wannan karo. domin baza mu ci gaba da zura ido tana cin zarafin 'yan uwan mu musulmai na kasar Palasdiwa ba".


"Mun fi so a yi yaki na duniya da mu zura ido ana kisan 'yan uwan mu musulmai a kasar Palasdiwa ba".


"Saboda haka a shirye mu da mu taimakawa kasar Palasdiwa ta hanyar kai hare-haren ramuwar gayya ga kasar Isra'ila matukar ta ci gaba da kai hare-hare".


"Babu wata kasa a wannan duniya da muke shakka ko jin tsoro akan kare martabar 'yan uwan mu musulmai a duk inda su ke a fadin wannan duniya". Inji Erdogan.


Erdogan ya yi wannan kakkausan gargadi ne a lokacin da ya kira taron gaggauta na shugabannin kasashen Larabawa don taimakawa musulman Palasdiwa.


Shin ya kuke kallon wannan mataki da Erdogan yake son dauka kan kasar Isra'ila?

Comments