Min menu

Pages

Ka saya min abaya bayan sallah zan baka kaina kayi duk abinda kaga dama inji wata budurwa

 Ka saya min Abaya bayan Sallah zan baka kai na ka yi duk abin da kake son yi da ni~ Wata BudurwaAkwai matsala fa...


Wata masifa ta shigo arewancin Nigeria ta Abaya


Na rasa sanin wannan dalilin da duk azumi sai an samu sabuwar masifar data shigo tayi gaba da imanin samari da 'yan matan mu.


Bana mantawa free call na MTN a watan azumi aka fara fitowa da shi, wanda yayi sanadin lalacewar mata dayawa da ba a san adadin su ba.


Kwatsam a wannan azumin sai ga masifar Abaya challenge ta shigo.


Abaya tun bamu da wayo mata suke sakata, amma a wannan shekarar saboda masifar Abaya challenge abin ya canja salon, ko ina Abaya Abaya. 


Wannan masifar data tunkaro na neman barazana ga iyayen yara mata da ma su kan su 'yan matan.


An bani wani screen shot na wata buburwa da wani saurayin ta akan cewa ya saya mata Abaya guda biyu bayan sallah zata sallama masa kanta yayi duk abinda yake son yi da ita.


Wannan kenan daya fito fili, Allah kadai yasan adadin wadanda suka kulla irin wannan yarjejeniyar.


Yanzu haka cinikin Abaya ya karu, mafi yawan masu saya samari ne da manyan banza masu 6ata tarbiyyar yafyan jama'a.


Saboda haka ina kiran iyaye da su Kara saka Ido sosai akan ya'yan su.


Sannan malamai a tashi ayi wa'azi ayi nasiha a jawo hankalin matasa akan wannan masifar data tunkaro mu.


Allah ya wargaza wannan masifar ta Abaya challenge.


Allah ya kawo Mana karshen wannan masifar dake addabar Arewa ciki da wajen kasar nan.


Allah ya shirye mu baki daya.


Comments