Min menu

Pages

Doka ta bamu damar tsige shugaban kasa matukar ya kasa yin wadannan abubuwan inji dan majalisa

 Doka ce ta ba mu Damar Tsige Shugaban Ƙasa Muddin Ba Zai Iya Kare Rayukan Jama'a Ba




Wani Ɗan Majalisa ya miƙe a Zauren Majalisar Wakilan Tarayya yana cewa, Zamu Tsige Shugaba Buhari Idan Matsalar Rashin Tsaro Ya Ci Gaba, Bayan Taron Tsaro A Wata Mai Zuwa.


Ɗan Majalisar da ke wakiltar Mazabar Tarayyar Jos ta Kudu da Jos ta Gabas a Majalisar Wakilai, Dachung Bagos ya ce Majalisar Dokoki ta Kasa za ta fara shirin tsige Shugaba Muhammadu Buhari idan tsaro ya Ci gaba da tabarbare a watan Mayu.


 "Kamar dai irin wannan binciken ne da Majalisar Dokoki ta ba fadar Shugaban kasa da bangaren zartarwa wadanda suka duba, har suka ce me kuke da shi, ku kawo shi kan teburi. A shirye muke mu amince muddin za ku magance matsalar rashin tsaro.


A tunani na Saboda Babu wani memba da abin ya shafa kai tsaye shi yasa muke wasa da lamarin rashin tsaron da ke ƙasar nan To ni yanzu abin ya kai ni ga ban ma iya zuwa mazaɓata saboda kashe-kashe nan da can.


Bagos ya ce "Idan har bangaren zartarwa ba zai aiwatar da komai ba bayan wannan mafaka ta karshe to muna kira da a tsige Shugaban ƙasa nan take, inji shi.


Domin Doka ta ce Muna da ikon tsige Shugaban ƙasa idan har ba zai iya ci gaba da tsare rayuka da dukiyoyin 'yan Najeriya ba.

Comments