Min menu

Pages

Idan har matanku sunada ciki to ku guji aikata musu irin wadannan abubuwan

 Idan har matanku sunada ciki to ku guji aikata musu irin wadannan abubuwanKamar yadda kuka sani ciki a jikin mace ba karamin abu bane yake zuwa da abubuwa ko kuma kalubale iri iri wanda ake da bukatar duk wasu maza da matansu keda ciki su zamto suna kula da kuma yin kaffa kaffa...


Domin wasu daga cikin maza ko kusa basa yin wani abu da zai sanya matarsa cikin nishadi da walwala in tana da ciki, wani sai kaga baya tashi takurawa matar tasa ma da masifa ko fada sai ta samu juna biyu wanda hakan kuwa matsala ne babba.


Domin akwai abubuwan da mata ke son ayi musu da zarar sun dauki ciki, wanda abin yanada matukar tasiri ga lafiyarsu harma ta abinda ke cikinsu.

Dan haka zamu kawo muku wasu abubuwa da za kuna yiwa matanku da zarar sun samu ciki.

Ga abubuwan kamar haka

√ Duka :- koda wasa karka gwada dukan matarka idan har tanada ciki ko kuma ka fada mata magana maras dadi, ana bukatar kana lallashinta tare da mata duk abinda take so.

√ Ka daina barinta ba bacci:- koda yaushe ana bukatar kana barinta tana samun bacci isashshe wanda hakan zai taimaka kwarai da gaske.


√ Ka daina daga mata murya ko yi mata kalamai marasa dadi wanda za su tashi hankalin ta koda yaushe ana bukatar kana saukar da muryarka idan za kayi mata kalamai


√ Aikin gida :- Idan da dama wasu ayyukan gidan ma kuna yi tare kana taimaka mata hakan zaisa abubuwa su tafi daidai.Comments