Min menu

Pages

Gaskiya ta fara bayyana game da faduwar jirgin da Shugaban sojoji yake ciki

 Gaskiya ta fara bayyana game da faduwar jirgin da Shugaban sojoji yake cikiTun bayyanar hatsarin da wani jirgin sama dauke da manyan sojojin yayi wanda cikinsa yake dauke da Shugaban sojoji Ibrahim Attahiru ake ta maganganu wasu ma saidai kawai mutane suyi shiru.


Jirgin daya fadi tare da kamawa da wuta wanda hakan yai sanadiyyar salwantar rayukan duka mutanen dake cikin jirgin ciki harda shugaban sojojin.


To saidai wasu shaidun gani da ido sunce sunga mutane biyu sun fado kasa ta hanyar amfani da umbrella lokacin da jirgin yake tangal tangal zai fadi.


Sunce a gabansu mutanen suka sauko saidai sun nemi inda mutanen sukai sun rasa amma tabbas sun gansu.

Idan ta tabbata haka ne kenan akwai wani abu game da mutuwar tasu.
Comments