Min menu

Pages

Neman mijin aure nake inji wata budurwa

 Neman mijin aure nake saidai in saurayi yasan bai cika wannan sharadin ba kar yazo guna inji wata budurwaWata hadaddiyar budurwa ta bayyana abinda yake ranta na sanar da duniya cewar aure take so to saidai ta fadi irin kalar mijin da take so.


Budurwar data bayyana sunanta a matsayin Aysha wacce ake mata inkiya da Ummi tace tana son aure saidai tafi son saurayi dan gayu.


Ni gaye nake so wanda ya iya wanka, wanda idan yasa kaya suke matukar yi masa kyau tare da zama a jikinsa a cewar budurwar.


Dan haka duk wanda yasan ya yarda da kansa yazo na tantance shi.

Comments