Min menu

Pages

Dubun wani matashi da yake yaudarar yan mata da sunan zai basu aiki ta cika bayan yayiwa wata fyade

 Dubun wani matashi ta cika da ya kware wajen shigar attajirai a social media yana gayyatar yan mata wajensa da sunan zai basu aiki sai sun je yayi masu fyade ya kashe su a jihar Akwa-IbomDubun wani matashi ta cika a jihar Akwa-Ibom da ya kware wajen yaudarar yan mata a dandalin sadarwa (social media) da sunan shi wani babban mai kudi ne yana gayyatar yan mata da nufin zai basu aikin yi amma sai sun je sai ya yi zina dasu ko yayi masu fyade sannan ya koresu ko kuma ya kashe su.


Matashin mai suna Uduak Frank Akpan, dubunsa ta cika ne bayan da ya gayyaci wata matashiya mai suna Ini-bong Umoren bayan ya ga ta rubuta a shafinta na Facebook da twitter cewa tana neman aiki sai ya gayyace ta da sunan zai bata aiki, ashe matashiyar ta rika  sanar da yan'uwanta tare da tura masu duk abunda ya shiga tsakanin ta da matashin kama daga lambobin da yake kiranta dasu har zuwa inda yace ta same shi duk tana tura masu ta waya.


Jaridar ta ruwaito jim kadan da matashiyar ta sanarwa yan'uwanta cewa ta karasa inda yake yace ta jira shi cen bayan yan mintuna sai ga kiranta yanuwan na dauka sai suka ji tayi ihun neman taimako sai kuma akaji wayar ya katse lamarin da yasa nan da nan yan'uwanta suka sanar da jama'a aka fara bibiyar wajen da tace take har dai dubun matashin ta cika aka gano yayi ma matashiyar fyade sannan ya kashe ta ya haka rami ya saka ta ya bizne.


Wata jarida ta ruwaito matashin ya shaidawa yan sanda bayan ya shiga hannu cewa ya dade yana wannan sana'a kuma mata dayawa ne suka fada tarkonsa.

Comments