Min menu

Pages

DA ƊUMI-ƊUMI: BABU AURE TSAKANINA DA SANI DANJA - MANSURA ISAH

 DA ƊUMI-ƊUMI: BABU AURE TSAKANINA DA SANI DANJA - MANSURA ISAHFitacciyar jarumar fina-finan Hausa ta Kannywood, Mansura Isa ta bayyana cewa a yanzu haka babu aure a tsakaninta da mijinta Sani Musa Danja wanda ya ke fitaccen jarumi ne shi ma a masana'antar Kannywood.


Wata jarida ta ruwaito Mansura Isan na bayyana hakan a shafinta na Instagram minti guda kafin ta goge rubutun.


A zantawar da mu ka yi da mijin nata, Sani Danja ta wayar salula, mun tambaye shi ko shin gaskiya ne sun rabu da matarsa Mansura Isah ? Sai ya amsa da cewa:"Ku je ku tambaye ta tunda ita ce ta rubuta". Cewar Sani Danja.


Sai dai kuma wata majiya mai tushe wacce ta nemi mu sakaya sunanta ta tabbatar mana da cewa auren na Sani Danja da Mansura Isah ya daɗe da mutuwa yau tsawon shekara guda kenan ba sa tare a matsayin miji da mata.


Sani Danja da Mansura Isah fitattun jarumai ne masu tashe a masana'antar Kannywood waɗanda su ka yi aure irin na soyayya tsawon shekaru kusan goma da su ka gabata. Yanzu haka su na da ƴaƴa hudu mace ɗaya da maza ukku waɗanda su ka haifa tare kafin su kai ga datse igiyar auren da ke tsakaninsu.


Har zuwa yanzu da mu ka haɗa wannan rahoto mun yi ta ƙoƙarin tuntuɓar Jaruma Mansura Isah ta wayar salula domin jin ta bakinta game da gaskiyar wannan lamari da ta rubuta ta goge amma ba mu kai ga nasarar samunta ba. Za mu cigaba da tuntuɓarta domin jin ta bakinta, ku cigaba da kasancewa da wannan shafin domin cigaba da samun ƙarin rahotanni kan wannan batu da ma sauran batutu kan lamuran yau da kullum.


Comments