Min menu

Pages

Mafusata Sun Kona Mahaukaciyar Da Aka Gano Bindigu Kirar AK 47 Guda Uku Da Sassan Mutane A Cikin Kayanta A Jihar Lagos

 Mafusata Sun Kona Mahaukaciyar Da Aka Gano Bindigu Kirar AK 47 Guda Uku Da Sassan Mutane A Cikin Kayanta A Jihar LagosAbun mamaki ba ya ƙarewa a duniya, an kama wata mata da sunan mahaukaciya a jihar Lagos a Unguwar Abule- Ado a yankin da ake kasuwar Duniya wato Trade fair Badagry.


Abun mamakin shine an samu wannan mahaukaciya da bindigu ƙirar Ak 47 har guda uku da kuma wasu sassan jikin dan Adam, wanda hakan ya sa jama'a ba su yi wata-wata ba suka banka mata wuta ta ƙone ƙurmus.


Bisa ga zargin da jama'a ke yi shine matar tana ɓoye bindigun ne domin masu fashi da makami dake yankin.


Kawo yanzu dai babu wani cikakken bayani daga jami'ai dangane da afkuwar lamarin.

Comments