Min menu

Pages

An kame wani mutum bisa zargin yi wa abokin kwanansa yankan rago ya saka gawar cikin buhu ya boye ta cikin wani daji.

 An kame wani mutum bisa zargin yi wa abokin kwanansa yankan rago ya saka gawar cikin buhu ya boye ta cikin wani daji. Wanda ake zargin dan shekara 34, ya fito ne daga Karamar Hukumar Ughelli ta Arewa a Jihar Delta. 


Mutumin da ya nemi kashe Limamin Masallacin Harami ya ce shi ne Mahadi

An kama mahaukaciya da bindigogi a Legas

Lamarin da ya faru a karshen mako a garin Sagbama an yi rufa-rufa kansa har sai bayan da matasan yankin suka gano gawar mamacin ta fara rubewa a cikin daji ranar Litinin.Koda yake hukumomin ’yan sanda a Jihar Bayelsa sun tabbatar da faruwar aika-aikar da ma kame wanda ake zargin, amma mutumin ya ki bayyana ko wane ne marigayin.


Mutane da dama a yankin sun ce sun yi amannar cewa mutumin ya kashe abokin kwanansa ne domin aikata tsafi, amma yawan ’yan banga a wajen ya hana shi fita da gawar. 


Bayan da ’yan bangar garin suka gano gawar a dajin ne suka ankarar da ofishin ’yan sanda na garin Sagbama, abin da ya haifar da kame wanda ake zargin. 


Kakakin rundunar ’yan sandan a Jihar Bayelsa, SP Asinim Butswat, yayin tabbatar da lamarin ya ce ana tsare da wanda ake zargin a Sashen kula da Manyan Laifuka na Rundunar domin ci gaba da bincike. 
Comments