Min menu

Pages

Zan dau fansar mahaifina da suka kashe inji dan gidan shugaban kasar chadi mahamat Idris dabby karin bayani

 Zan dau fansar mahaifina da suka kashe inji dan gidan shugaban kasar chadi.


Karaanta:- Allah sarki yadda matar shugaban kasar chadi ta fashe da kuka a wajen jana'izar mijinta

Dan gidan shugaban kasar chadi mahamat Idris dabby kuma shugaban kasar chadi a yanzu yace zai dauki fansar mahaifinsa da aka kashe.


Yace indai da numfashi a kirjinsa to dole sai ya dauki fansar kisan da akaiwa mahaifinsa inji mahamat din.


Muna sane da yan tawayen da suka zama ajalin mahaifina kuma bazan ragar musu ba da ikon Allah sai naga bayansu inji dan gidan shugaban kasar chadi idris dabby.


Tun shekaran jiya aka samu wasu yan tawaye sun kashe shugaban kasar chadi ta hanyar harbinsa da bindinga wanda hakan yasa rai yayi halinsa wanda jim kadan da mutuwar shugaban kasar aka nada dansa a matsayin shugaban kasar.


To saidai tun bayan da akai jana'izar mahaifin nasa yau mammat din yace sai ya dauki fansa akan su mahadi Ali wanda shine shugaban daya jagoranci kashe mahaifin nasa.


Mahadi Ali shine shugaban kungiyar FACT wacce ta kashe idris dabby na chadi.


Saidai mahamat idris dabby yace in har yana raye bai mutu ba to da ikon Allah saiya dauki fansa.

Comments