Min menu

Pages

Na daina tattaunawa da yan bindinga saboda wadannan dalilan Inji Gumi

 Na Daina Tattaunawa Da Ƴan Bindiga - Sheikh Ahmad GumiShehu kuma fitaccen malamin addinin Islamar nan da ke a Kaduna Sheikh Ahmad Gumi, ya ce ya daina tattaunawa da ƴan bindigar da ke addabar jihar saboda gwamnatin jihar ba ta da sha'awar yin hakan.


Da yake magana da wata kafar yaɗa labarai a ranar Alhamis, mai taimakawa Sheikh Gumi kan harkokin yaɗa labarai, Salisu Hassan, ya ce malamin ya dakatar da shirinsa ne domin mutunta shawarar da gwamnatin jihar ta yanke.


Idan za a tuna Sheikh Gumi ya ratsa dazuzzuka da yawa a yankin Arewa maso Yamma don haɗuwa da ƙungiyoyin ƴan fashi don yi musu wa'azi, matakin da Gwamna Nasir El-Rufai ya ƙi amincewa da shi.


Gwamnan ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar ba za ta shiga cikin masu aikata miyagun laifuffuka ta kowace irin tattaunawa ba, ya na mai cewa waɗannan ƴan ta'addan sun cancanci kashe wa, ba wai ai masu afuwa ba.Comments