Min menu

Pages

Yan tawayen da suka kashe shugaban kasar chadi zasu fuskanci fushinmu inji Buhari

 Muna Allah wadai da kisan shugaban kasar chadi da yan tawaye sukai.Hakika munji rashin dadi game da wannan danyen hukuncin da yan tawaye suka yanke a kasar chadi na kisan shugaban kasar.


Kuma muna sanar dasu su kuka da kansu zamu dauki mataki akansu mafi munin mataki mu kasashen dake makotaka da kasar chadin inji shugaban kasar Nijeriya Muhammadu Buhari.


Wannan kisan ba iya yan kasar chadi ne kadai sukai rashi ba harda sauran kasashen domin jagoran da aka kashe mai kokari ne sosai wajen yaki da yan ta'adda masu tada kayar baya.


Dan haka mu sauran kasashen dake makota da kasar ta chadi baza mu lamunta ba dole zamu hada karfi da karfe mu yaki wadannan da sukai silar mutuwar tasa.

Comments