Min menu

Pages

Wani dan sarki yayiwa Budurwa cikin shege a sokoto

 Wani dan sarki yayiwa Budurwa cikin shege a sokotoAna zargin wani matashi da ba'a bayyana sunan sa ba dan gidan sarkin karamar hukumar mulkin Tureta a jahar sokoto da  tuhumar dinkirawa budurwa mai suna Rakkiya cikin shege har juna biyu.


Rakkiyar ta yi bayani dalla-dalla kan yadda lamarin ya afku, tace bada son ranta aka yi lalatar da ita ba.


Ta bayyana cewar, tana sana'ar sayar da fura da Nono ne sai mutumen yayi barazanar yin lalata da ita ko ya illatata, daga nan ta nuna bukatar yayi lalatar da ita akai-akai gudun kar ya kashe ta: inji ta


Haka kuma ta bayyana cewar, matashin yayi kokarin a zubar da cikin biyo bayan tabbatar da cikin nasa na juna biyu ne.


Budurwar ta bayyana cewar, mahaifanta sun kasa kai kara a gaban koliya gudun kar sarkin garin ya koresu daga garin.


Yanzu haka dai, matashiyar tana samun kulawa daga kungiyar NAPTIP Kungiyar dake kwatowa mata Hakkokan su.Comments