Min menu

Pages

Wani dalili yasa mahaifi ya kashe dansa a Kano

 Wani abin mamaki ya faru da mahaifi ya zama sila wajen mutuwar dansa a jihar kanoHukumar yan sanda ta jihar kano tace ta kama mahaifin wani yaro ranar laraba bisa zarginsa da laifin kashe dan nasa dan shekara goma sha tara ta hanyar dukan da yai masa da ice saboda yayi sata.


Yan sandan sunce mal Awaisu yayi amfani da itace ne wajen dukan dan nasa saboda ya aikata sata wanda hakan yakai ga mutuwar yaron bayan an kaishi asibiti da gaggawa anan rai yayi halin nasa.

Mai magana da yawun yan sandan jihar kanon DSP Malam Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar wannan lamarin inda yace hakika an mahaifin da ya daki dan nasa da ice wanda yai sanadin mutuwar yaron.


Yace a ranar 27 ga watan March muka samu labarin cewa mal Awaisu dan kimanin shekaru arba'in da haihuwa da suke zaune a unguwar samegu yayi amfani da ice wajen dukan dan nasa mai suna Auwal dan shekara goma sha tara wanda yai sanadiyar mutuwar sa.


To anyi saurin kaishi asibiti na murtala dake kanon to amma rai yayi halin nasa.


Daga karshe dai shugaban hukumar yan sandan ya tura case din gurin masu kula da irin wadannan munanan laifukan domin ayi bincike.


Duniyar labarai


Comments