Min menu

Pages

Mun kusa mu fara kawo manyan hare hare Arewa inji mayakan biafra

 Yan arewa ku shirya yadda zaku kare kanku daga hare haren da zamu fara kawo muku



Ku saurare mu, domin nan da wani Lokaci 'Kan'kane za mu dira yankin Arewa inji kungiyar mayakan 


Kungiyar mayakan rajin kafa Kasar Biafra wato-IPOB, ESN ta bayyana cewa nan bada jimawa ba, za su dira yankin Arewa domin fadada ayyukan su.


Wannan ya biyo wani martani da Kungiyar ta fitar game da wani zargi wai Kungiyar Miyetti Allah za su shigo da wasu yan uwan su mutum dubu 5000 domin taya su samar musu kariya da tsaro daga Kungiyar ESN dake kai musu hari.


Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa a wannan takarda wanda Mai Magana da yawun kungiyar Emmanuel Powerful ya sa wa hannu, ya ce ” Shege ka fasa", suna jiran wadanda ‘Yan kungiyar Miyetti Allah za su shigo da su yankin domin sai sun rai na kasu.


” Wannan abu cin fuska ne ga mu Inyamurai, amma kuma ina so in sanar musu cewa muna nan muna jiran su su shigo su gani. Ba jiran su ma kawai muke yi ba, ita kanta yankin Arewan su sauraremu muna nan dirowa yankin".


A rahoton da muka samu, ya nuna cewa Yankin Kudu maso gabas, sun kirkiro wata kungiya mai suna ESN.


Wanda ake zargi da bi bin rugagen fulani suna babbakewa, inda suke cewa wai su tattara su fice musu daga yanki.


Haka Zalika, ana zargin su da kashe yan Arewa a hare-hare da dama da suke kaiwa a yankin.

Comments