Min menu

Pages

An bayyana sunayen mutanen dake turawa yan boko haram kudi

 An bayyana sunayen mutanen dake turawa yan boko haram kudi.


Gwamnatin tarayya ta bayyana sunayen wasu yan canji da tace sune ke turawa yan boko haram kudi.


Gwamnatin ta sanar da hakan ne daga bakin mai magana da yawun gwamnatin garba shehu inda tace masu turawa yan boko haram din kudi mafiya yawa yan canji ne da masu sayar da gwala gwalai.


Yace wasu yan Nijeriya dake zama a daular labarawa suke aiki da yan canji sune ke turawa yan boko haram din kudi.


Daga cikinsu akwai baba hussain da kuma Abubakar yellow da Ibrahim shani da yusuf ali dadai sauransu.Comments