Min menu

Pages

An kashe soja biyar da wasu mutum biyu

 Yan bindinga sun kashe sojoji biyar tare da wasu mutane biyu a garin karamar hukumar Shiroro dake jihar Niger.Ko ranar laraba data shige an samu labarin yadda yan bindingar suka sace mutum goma sannan sukai awun gaba da abin hawa guda bakwai tare da kone wasu motoci na jami'an tsaro a akwa ibom.


To yanzu ma ta sake faruwa inda yan bindingar suka kutsa kauyukan Allawa,gurmana, bassa da kuma manta da kokki dake karamar hukumar Shiroro ta jihar Niger.


Majiyar tace yan bindingar sun rufarwa guraren da hadakar jami'an tsaro suke na civil defense da sojoji da yan sanda da kuma yan banga sun bude musu wuta kai tsaye.


Wani daga cikin babba na jami'an civil defense yana daga cikin wanda aka kashe kuma aka jiwa wasu da dama ciwo.


Mazauna yankin sunce hakika yan bindingar sun shigo garin manta da Gurmana Bassa harma sun kashe wani ana kiransa Alhaji sule.


A kalla yan bindingar sunkai mutum dari sannan suna rike da manyan bindigu kirar AK47 inji mutanen yankin.

Comments