Min menu

Pages

Yadda ta fara aman jini bayan an mata allurar rigakafin korona

 An bayyana wata ta fara aman jini bayan da akai mata allurar rigakafin korona a Kaduna.Wata mazauniyar jihar Kaduna mai suna hannatu ta bayyana yadda ta fara zubar da jini ta hanci sannan ta fara aman jini tun lokacinda akai mata allurar rigakafin korona.


A wani faifan bidiyon da yake yawo online anga lokacin da ake mata aiki a wani asibitin kwararru dake kaduna.


Matar tace an mata allurar ne a kadunan sannan an kwantar da ita kwana shida bayan ta karbi allurar.


To saidai babba daga cikin mutanen asibitin da aka kwantar da ita yace bai dace ana watsa bidiyon ba saboda sudai an kawo ta asibitin ne kuma ance an mata allurar wajen kwana shida.


Har ya sake cewa su duka anyi musu wannan allurar amma babu wani abu daya faru.


To idan baku manta ba dai allurar rigakafin korona kusan mutane dama basu gaskata ta ba haka wasu kasashen ma domin sun hana a shigo da ita.

Comments