Min menu

Pages

An kammala daukar shirin film din Labarina ko kunsan yaushe za a fara nunashi?

 An kammala daukar shirin film din Labarina zango na uku..Hadadden shirin film din nan mai dogon zango na kamfanin saira movie wato labarina an kammala daukarsa yanzu sai nunawa ce kawai ta rage.


Mutane sun kagu su san lokacin da za a fara sakin wannan kasaitaccen shirin, hakan yasa muka tuntubi masu ruwa da tsaki a shirin domin muji ko yaushe zasu fara haska shirin.


To saidai Daraktan shirin Malam Aminu saira ya shaida mana cewar yanzu wata ne na Ramadan yake shirin kamawa wanda bazai iyu a fara haska shirin cikin wannan watan ba domin wata ne na ibada wanda ake bukatar mutum ya dage da aikata aikin lada a cikinsa.


Sannan ya kara da cewa shirin za a fara nunashi ne a matsayin goron sallah dan haka masu kallo su jira zuwa bayan sallah.


A ina za a fara haska shirin?

Mutane suna ta tambayar wai an daina haska shirin a tashar arewa24 idan an daina haska shi to a ina kenan za ana haskawa?


Malam Aminu saira sai yace ba daina haska shirin akai cikin tashar arewa24 ba adadin shirin da mukai alkawari da tashar ne ya kare domin dama zango na daya dana biyu ne mukai alkawari dasu kuma sun kare, dan haka yanzu mun dauki na uku idan mun shirya dasu shikenan za muci gaba da dora musu a tashar idan bamu shirya ba shikenan zamu sanar da inda za muna dorawa idan lokaci yayi.Comments