Min menu

Pages

Lagos: Farashin Rago ya kai naira miliyan ɗaya a


 Lagos: Farashin Rago ya kai naira miliyan ɗaya a kasuwar Alaba saboda yajin aikin masu kayan gwari



Yajin aikin haɗaɗɗiyar Kungiyar masu kayan gwari da cimaka ta ƙasa ya haifar da tsadar farashin kayayyakin musamman kayan abinci da dabbobi a kudancin Najeriya.


An nuna wa News World Hausa wani Rago da farashinsa ya kai naira miliyan ɗaya, wani kuma ya kai naira dubu 800k.


Tun a makon jiya ne ƴan kasuwar dake kai kayan abinci kudancin Najeriya daga yankin arewaci suka fara yajin aikin.


Sun shiga yajin aikin ne domin nuna goyon baya ga ƴan uwansu mutanen arewa da rikicin kasuwar Sasa ya shafa a garin Ibadan na jihar Oyo

Yanzu yajin aikin ya yi tasiri bayan haifar da tsadar farashin kayayyakin abinci a yankin kudu maso yammacin Najeriya.


Har yanzu hukumomi ba su ce komai ba game da yajin aikin haɗaɗɗiyar ƙungiyar ta masu kayan gwari da kayan abinci.


Koda yake ɗaya daga cikin shugabannin ƙungiyar yace za suyi zama da wakilan gwamnatin tarayya a fadar shugaban ƙasa a ranar Talata.

Wakilin News World Hausa Mustapha Isa  ya ziyarci kasuwar Alaba a Legas kuma ya ce kasuwar ta zama fayau.


Farashin kayayyaki sun lunka kusan sau uku sakamakon yajin aikin.


Tanimu Bulama Wazirin Sarkin Alabar Rago kuma shugaban masu sauke dabbobi a kasuwar ya ce an taya wani ragonsa dubu 950k bai sayar ba.


Yan kasuwar sun ce kusan yawancin ragunan da su ke kaiwa kudancin Najeriya ana kawo su ne daga Sudan da Nijar.


Kaji da ake sayarwa N1,500 yanzu sun koma N2,500 sakamakon yajin aikin da ya haifar da ƙarancin kajin.


Ɗaya daga cikin ƴan kasuwar Alaba a ɓangaren kaji Muhammadun Dauran Kaji ya ce yanzu Talo-Talo har naira dubu 30 ake sayar da shi.


Muhammadu Aminu mai kayan gwari ya ce albasa da ake sayarwa N12,000 yanzu ta koma dubu 30k kwando.


Tumatur kuma da ake sayar wa naira hamsin yanzu sai dai kusan 300k.


Abin da ƴan kasuwar suka ce kan yajin aikin


Shugabannin kasuwar sun ce suna yajin aikin ne domin neman wa ƴan uwansu ƴancinsu.


Sarkin kasuwar Alaba rago, Alhaji Umaru na Goggo ya musanta cewa an ɓoye kayyakin ne don a tsawalla farashi.


Ya kuma ce ko za a janye yajin aikin sai kungiya ta yi zama ta yi nazari kafin janye aikin.


"Sai mun yi zama da waɗanda abin ya shafa musamman jigogin gwamnati mun zauna da su a yi wa kafin kungiya ta amince a janye yajin aikin."


Sarkin kasuwar kuma yayi kira ga Gwamnatin Najeriya ta shiga tsakani ta yi bincike domin gano wadanda ke da gaskiya da kuma daukar mataki kan wadanda ke saɓa doka.


Tanimu Bulama Wazirin Sarkin Alabar rago shugaban masu sauke dabbobi a kasuwar ya ce baya ga nuna muhimmancin amfanin kasuwancinsu na kayayyakin abinci da suke kawo a kudanci suna kuma son a ɗauki mataki kan kuɗaden da ake tatsa daga gare su.


"Muna neman wa mutanenmu ƴancinsu ne kuma dole mu ba su yi hakuri su jure har lokacin da za a dadaita wannan al'amarin," in ji shi.


Ya ƙara da cewa wannan gargaɗi ne saboda fahimtar amfanin masu kawo kayan abinci a yankin kudancin Najeriya.




Zauren fiqhus sunnah
Zauren fiqhus sunnah
BARKA DA ZUWA WEBSITE DINMU NA-- DUNIYAR LABARAI MUNA SANAR DA MASU SHIGA WANNAN SHAFI CEWA ZAMU CIGABA DA FADAKARWA ,DA ILMANTARWA INSHA-ALLAH Phone Number 08084396103 Email Zaurenfiqhussunah@gmail.com

Comments