Min menu

Pages

Jam'iyyar PDP ta kori dan takarar gwamna na Jihar Jigawa daga cikinta bisa wannan dalilin

 Jam'iyyar PDP ta kori dan takarar gwamna a shekarar 2015 Mal Aminu Ringim daga jam'iyyar gaba daya.Jam'iyyar ta PDP ta kori dan takarar gwamna na jihar jigawa Malam Aminu Ringim bisa zargin sa da kin bin umarnin jam'iyyar PDP din.


An yanke wannan hukuncin ne jiya bayan wani zama da yan jam'iyyar suka gudanar a Birnin Dutse Jihar Jigawa.


Organizing secretary na jam'iyyar Babangida Muhd Roni yace sunbi duk wasu matakai da kuma ka'idojin da dokar kundin tsarin jam'iyyar PDP din ta fitar da ita sukai amfani wajen korar Aminu Ringim din saboda dokar daya karya.


A da can Mal Aminu Ibrahim Ringim shine dan takarar jam'iyyar PDP a Jihar Jigawa bisa jagorancin Sule Lamido, saidai a yan kwanakin baya an samu takun saka tsakanin sa da shugaban tafiyar nasu sule lamido wanda hakan baizo da dadi ba.


Wannan tasa har kowa ya kama nasa bangaren.

Comments