Min menu

Pages

Zamu bude Duk kan iyakokin da Buhari ya rufe na yankin mu domin yanzu mu ba yan kasar sa bane inji Sunday Igboho

 Zamu bude Duk kan iyakokin da Buhari ya rufe na yankin mu domin yanzu mu ba yan kasar sa bane inji Sunday Igboho.Shugaban masu fafutukar kafa yankin yarabawa Sunday Igboho yace duk saiya bude iyakokin da Buhari ya rufe lokacin da suke cikin kasar Nigeria saboda yanzu su ba yan kasar bane.


Yace da kam an garkame musu iyakokin ne kuma sunyi hakuri duk da bawai dan suna so bane, amma yanzu kam dole da kaina zan bude wadannan iyakokin tunda mun koma masu cin gashin kanmu.


Sunday Igboho ya dage sosai kan batunsa na lalle sai sun fita daga kasar Nijeriya shida sauran yan uwansa yarabawa domin suma su gina sabuwar kasarsu.


Ko a yan kwanakin nan an samu bayyanar wasu photuna na kudi wanda suka fitar wai na yan kasar yarabawa ne domin dasu za suna yin amfani sun daina amfani dana kasar Nijeriya a cewarsu.Tsarin da wasu yankuna suka bi wajen cewa sai an fitar dasu daga cikin kasar Nijeriya wata matsala ce da ya kamata mahukunta su zuba ido akai domin shawo kan matsalar.

Comments