Min menu

Pages

An baiwa Makiyaya Sati Biyu su bar Jihar Ekiti

Gwannatin Jihar Ekiti  Ta Bawa Makiyaya Wa'adin Makwanni 2 Su Yi Rajista Ko Su Tattara Su Bar Jihar


Jihar Ekiti a kudanci ta baiwa makiyaya da manoma wa'adin makwanni 2 su yi rajista a Jihar ta Ekiti ta kuma gargadesu da cewa kin yin hakan zai sa a fatattake su a fadin jihar - 


Tuni dokar ta fara aiki a yau Litinin 22 ga watan Maris, daga majiya mai tushe na jihar Gwamnatin jihar Ekiti a Kudu maso gabashin Najeriya ta ba wa'adin mako biyu ga makiyaya da manoma a fadin jihar cewa su yi rijista da gwamnatin jihar ko kuma su tattara nasu ya nasu su fita daga jihar baki daya. Tuni sanarwar ta bayyana wa'adin ya fara aiki tun ranar Lahadi, 22 ga watan Maris, BBC Hausa ta rahoto. 


Cikin wata sanarwar kwamishinan aikin gona da wadatar abinci na jihar Dakta Olabode Adetoyi, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta lura cewa rikici tsakanin manoma da makiyaya na haifar da hadari ga lafiyar mutane da kuma kokarin wadata jihar da abinci. 


Don haka daukar matakin rajistar ya zama wajibi ga gwamnati, don dakile matsalar rikici da ke ballewa tsakanin makiyayan da manoma.

 

Zauren fiqhus sunnah
Zauren fiqhus sunnah
BARKA DA ZUWA WEBSITE DINMU NA-- DUNIYAR LABARAI MUNA SANAR DA MASU SHIGA WANNAN SHAFI CEWA ZAMU CIGABA DA FADAKARWA ,DA ILMANTARWA INSHA-ALLAH Phone Number 08084396103 Email Zaurenfiqhussunah@gmail.com

Comments