Min menu

Pages

A kalla mutane 40 aka kashe a janhuriya Nijar

 A kalla mutane 40 aka sake kashewa a janhuriyar Nijar.Inda abin ya faru ne kusa da iyakar Nijar da kasar Mali.


Me magana da yawun gwamnatin abdulrahman zakariyya yace an tura jami'an tsaro can wurin da abin ya faru domin tunkarar wadanda sukai wannan aikin.


Ana yawan samun mahara ko kuma yan ta'adda dake yawan shiga Nijar da kuma sauran kasashen dake zagaye da kasar kamar Nijeriya da sauran su wasu suna ikirarin yan alqa'ida ne.


Ko a ranar sha shida an samu an kashe mutane wajen hamsin da takwas a Tilleberi ta cikin kasar nijar.Comments