Min menu

Pages

Za ayi ruwan wuta ga yan bindingar dake cikin daji.Daga karshe dai an yanke matsayar za ayiwa duk kan yan bindingar dake cikin daji ruwan wuta.


Baza a ragawa duk wani da yake cikin daji ba dan haka duk wani da aka gani yana rayuwa a jeji yanzu da ake cikin matsalar ta'addanci da rashin tsaro to dan bindinga ne.


 Jagora ko kuma shugaban hafsun sojoji na Nijeriya Lucky Irabor yace yanzu haka dakaru sun shirya tsaf domin shiga daji suyiwa yan bindingar luguden wuta.


Da yake magana a wajen wani taro da akayi a Abuja yace yanzu haka sun riga sun bankado duk wasu da suke buya a cikin daji suna kai hare hare.


Shugaban sojojin yace ta wannan luguden wutar ne kawai za'a kakkabe duk wasu dake rayuwa a jeji suna takurawa mutane.


Haka zalika in mukai haka muna fatan matsalar tsaron zata kare.


Haka zalika gwamnan Jihar Katsina ma ya sake bada sanarwa irin wannan cewar sojojin za suyi ruwan wuta ga duk wani jeji mafakar yan bindingar.

Comments