Min menu

Pages

Kwana biyu muka baka ko ka rage kudin siminti (cement) ko mu tattare duk kan wasu hanyoyi wata kungiya ta gargadi Dangote

 Ko ka rage kudin cement ko kuma mu hana safarar simintin a fadin kasar Nijeriya.Wata kungiya ta matasan kasar Nijeriya NISYA ta gargadi Dangote cewar ya rage farashin kudin siminti nan da kwana biyu.


Kungiyar ta koka matuka inda tace siminti yayi tashin goron zabi daga dubu biyu har zuwa dubu hudu a wasu yankunan ma dubu shida.


Kungiyar tace kudin yayi matukar yawa kuma suna bukatar Dangote da sauran masu yin siminti a kasar su rage kudinsa.


Sunce yanzu gini nema yake yafi karfin mutane musamman talakawa wanda suke samun taro sisi.


Akwai abin mamaki kayan da a kasarmu ake yinsa amma yana neman ya gagaremu a cewar kungiyar matasan.


Dan haka muke kira da babbar murya akan ayi kasa da farashin simintin nan da kwana biyu ko kuma mu tare duk wasu hanyoyin da ake kawo simintin.Comments