Min menu

Pages

Yan fashi sun kutsa kai cikin wani banki

 Wasu yan fashi sun kutsa kai cikin wani banki sun kwashe kudade masu yawa.Al'amarin ya faru ne a jihar Delta inda yan fashin sukai nasarar kutsa kai cikin bankin kai tsaye suka samu ma'aikatan bankin tare da mutanen da suka je bankin a ranar.


Sun dira bankin ne lokacinda ake harkoki wanda hakan yasa suka jima suna ta'asa a bankin.


Yan fashin sun kasu ne gida gida a cikin bankin kamar yadda saidun gani da ido suka tabbatar wanda hakan yasa sukai ta daukar kudaden mutane ba tare da wani matsala ba.


Ma'aikatan bankin basu samu damar yin wani abu ba saboda tsare sun da yan fashin sukai da bakin bindigogin dake hannunsu.


Wadanda suka tsaya a waje basu shigo ba daga cikin yan fashin sun bude wuta kan me uwa da wani inda har suka bindige wani har lahira.


A kalla an shafe wajen awa ana fashin ba tare da anga zuwan jami'an tsaro ba wanda hakan ya bada mamaki.

Comments