Min menu

Pages

Wata budurwa ta hada baki da sabon saurayinta sun kashe tsohon saurayinta akan wannan dalilin

 Wata budurwa ta kashe tsohon saurayinta.Al'amarin ya faru ne a jihar sokoto inda wata budurwa suka hada baki da sabon saurayinta suka kashe tsohon saurayinta.


Budurwa tare da saurayi da kuma sauran mutane biyar sun shiga hannun yan sanda dumu dumu bisa kashe wani bawan Allah da sukayi.


Mutumin da wannan budurwa da sabon saurayinta da suka kashe sunansa Abba Abbey kuma yana zaune ne cikin unguwar gidan haki dake cikin garin Sokoto.


Ana zargin budurwa da hada baki da sabon saurayinta wajen kisan tsohon saurayin inji wata majiya mai tushe.


Budurwar mai suna fatima sun taba yin soyayya da abba na wani lokaci amma suka rabu.


Bayan wani lokaci sai ta sake sabon saurayi wanda har takai ga maganar aure saidai a lokacin bata da kudi dan haka taje gun tsohon saurayin nata Abban kenan domin ya bata kudin kasancewarsa dan siyasa saidai a lokacin bata samu kudin ba a gareshi.


Daga karshe dai sukai wata shawara da sabon saurayin nata suka sace tsohon saurayin domin su nemi kudin fansa.


Dan haka saita kira tsohon saurayin nata a ranar da lamarin zai faru akan tana so su hadu a wani guri, lokacin da yaje saiya iske su tare da wani saurayi wanda tace dan uwanta ne kuma tace tana so ne ya kaisu wata unguwa a motarsa.


Bayan sun shiga suna tafiya suka nuna wani lungu bayan sun shiga inda motar bazata iya shiga ba dan haka sai yai nufin juyawa ya koma da baya amma sai yaga wata motar ta rufe bayan wasu sun fito kawai sukai gaba dashi bayan sun nuna masa bindinga.


Daga karshe dai sai gawarsa aka tsinta inda wasu abokansa suke cewa a daren da al'amarin ya faru ya kikkirasu akan su bashi aran kudi watakila su zai bawa da bai samu bane kawai suka kashe shi.
Comments