Min menu

Pages

Wasu manyan abubuwa da yankin yarabawa zasu rasa idan suka kuskura aka raba kasar nan

 Wasu abubuwa masu amfani da yan kabilar Yoruba zasu rasa idan suka kuskura aka ware su daga Nijeriya.



Yan kabilar Yoruba sun dage su a dole sai an raba su ko kuma an ware musu kasar su ta ododuwa.


Sunday Igboho da sauransu basu da magana saita a cire su daga cikin Nijeriya suma su kafa sabuwar kasarsu.


To saidai masu bincike sunce muddin yan kabilar Yoruba suka yarda aka raba kasar nan aka ware su to kuwa zasu rasa manyan abubuwa.


√ Abinci:- Abinci yana daya daga cikin abinda yankin yarabawa zai rasa da zarar an ware su daga Nijeriya domin daga yankin arewa ake shigar musu da abinci dan haka daga zarar an ware su to wannan abincin zai musu wuya sosai.

√ Nama :-  Bincike ya nuna duk wani nama da ake ci a yankin yarabawa na daga raguna ko awakai daga arewa ake kai musu dan haka ba karamar rashi za suyi ba daga zarar an ware su domin kuwa nama ma a karshe zaiyi musu wuya.

√ Danyen Mai dama can mai ba daga bangaren su yake ba dan haka daga zarar an ware su to kuwa zasu fara shan wahala na neman mai domin sai sunzo kasar Nijeriya sun saya ko wata kasa.


√ Kayan miya iya kayan miya ma ya ishe su aiki daga zarar an raba kasar nan an ware su domin duk wani kayan gwari daga nan arewa ake kai musu.


√ Tsaro akwai wahala su iya tara mayaka ko jami'an tsaro dan haka daga zarar an ware su to tsaro ma zaiyi musu wuya domin baza su samu damar kare kansu ba.


Wannan sune kadan daga cikin abubuwan da zasu rasa.

Comments