Min menu

Pages

Tura takai bango yan Npower sunyi zanga zanga a Abuja

 Yan Npower sunyi zanga zanga a AbujaMa'aikatan Npower sunyi zanga zangar ne biyo bayan alkawarirrikan da aka daukar musu wanda har yau ba a cika musu ba.


Ma'aikatan sun koka na ganin an jefar dasu a wannan tafiyar.


Sannan sun ce wasu daga cikinsu suna cine kuma su sha daga wannan aikin da aka dakatar dasu wanda tun daga lokacin da aka tsayar dasu daga aikin da yawa daga cikinsu basa samun wasu kudaden da za su biya bukatar su.


Wasu ma basa iya ciyar da iyalansu sau uku a rana.


Bayan haka gwamnati ta sanar da cewa akwai kudin da zata basu amma har yanzu shiru koda yaushe saidai a rika saka musu rana amma shiru.


Wannan yasa suka fito wannan zanga zangar domin gwamnati ta taimaka ta saka baki a biyasu wannan kudin da akai musu alkawari.

Comments